Akwai wasu abubuwa biyar da aka haramta a wasu kasashen duniya, amma a nan kasar Amurka dai-dai ne amfani dasu. Na farko, dukar yara dalibai babban laifi ne a wasu kasashen duniya; a nan kasar Amurka, jihohi goma sha tara ba su yadda da dukar yara ba. A wasu kasashen koda iyaye ba su da izinin dukar ‘ya'yansu. Kasar Sweden tana daya daga cikin kasashen da su ka hana dukar yara a shekarar 1979.
Na biyu, wasu sinadarai guda biyu, da ake samu a kowane irin abinci a duniya, da ake kiran su “hydroxyanisole” da “hydroxytoluene” a kalla a kasashe sama da dari da sittin (160), sun haramta barin wadannan sinadaran a cikin duk wani abincin sayarwa. Amma a kasar Amurka, duk wanda ke da bukata na iya saya.
Na uku, a kasar Singapore, a shekarar 1992, haramun ne a kama mutun ya na cin cingam, ko a gan shi ya na saida cingam na Bazooka, duk dai da cewar sun ce ba su na fada da motsa jiki ba ne, a’a; su damuwarsu ita ce, irin sinadarai da suga da ake sawa a ciki. Shi ne ya sa su ka dauki wannan matakin. Amma yanzu haka idan ka kawo cingam wanda ba shi da suga, za a iya barin ka ka shiga da shi cikin kasar.
Na hudu, a kasashe kamar su Denmark, New Zealand, da Sweden, da dai sauransu, akwai doka kan irin sunan da za ka sa ma yaro ko yarinya. Akasari dole ne iyaye su saka ma ‘ya'yansu suna daga cikin jerin sunaye dubu bakwai (7000) da gwamnati ta amince da su. Idan kuwa ka sa wani suna, ba daya daga cikin sunayen da gwamnati ta yarda dasu ba, to za ka hadu da fushin hukuma. Har kuwa idan ka na son wani suna, kuma baya cikin jerin sunayen da gwamnati ta amince da su, to sai dai mutun ya je coci, don neman izini. A kasar New Zealand kuwa, a duk shekara a na fitar da jerin sunaye da aka yadda mutun ya sa ma ‘ya'yan shi. A kasar Amurka, kuwa mutun ma na iya sa ma danshi suna shege, babu ruwan kowa da shi.
Na karshe kuwa, a shekarar 2006 ne wata mujallar kasuwanci ta ayyana kasar Bhutan, a matsayin kasar da tafi kowace kasa jin dadi a yankin kasashen Asia, kana kuma ta saka ta cikin kasa ta takwas 8, da ta fi kowace kasa jin dadi a duniya. Bayan shekara hudu, a kasar aka fito da wata doka, da ta kara ma manoman taba karfin gwiwa, da tallafi wajen kara yawan noman taba don kaiwa kasashen waje, amma a kasar haramun ne a kama mutun ya na zukar taba. Sun dai yadda su noma su kai wasu kasashen, amma muddun ka sha taba wani ya gan ka to za ka fukanci fushin hukuma.