Wasu abubuwa biyar da aka haramta a wasu kasashen duniya, amma a nan kasar Amurka, halas-malas ne. Na farko, a kasar Canada a shekarar 2004, gwamnati ta haramta koya ma yara tafiya, da wata keken koyon tafiya. A cewar su, wannan keken koyon tafiya, ga yara na da hadari ga rayuwar su matuka. Duk iyayen da aka kama su, suna amfani ma yaran su wannan keken za’a cisu tarar dallar Amurka $100,000 dai-dai da naira milliyan ashirin 20,000,000.
Na biyu, a shekarar 2005, a kasar France, an hana yima yara amfani da wani tumaturin gwan-gwani da ake kira “Ketchup” a turance. Wanda a nan kasar Amurka, idan akace yaro bazai ci wannan tumaturin ba, to lallai yasabama al’adun kasar Amurka. A cewar kasar bama yara tumaturin ya saba ma al’adun su.
Na uku, kasar Cuba, itace kasa ta farko da ta haramta amfani da fitilar kwai, a shekarar 2005, daga nan sai kasar Argentina, a shekarar 2010, kana kasashen yankin turawa, suma suka haramta amfani da ita fitilar kwai a shekara 2012.
Na hudu kuwa, a kasar Amurka, kowa na da hakkin yima gashin kanshi yadda yake so, namiji ko mace. Amma a kasar Iran, a shekarar 2010, sun saka wata doka da kuma ka’idoji da kowa sai yabi wajen gyaran gashi, mussamman ga maza, basu da damar yin aski irin na kasashen turawa.
Kana na biyar, kasar Bangladesh, itace kasa ta farko da ta haramta amfani da leda wajen zuba abubuwa, a shekarar 2002, daga nan wasu kasashe a duniya, suma sukabi sahu. Kasashe da suka hada da Tanzania, Mexico, harma da wasu jihohi a kasar Amurka sun hana amfani da laida bagi domin kuwa tana da hadari ga yanayin kasa.