Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba'Amerikiya Tazabi Zama 'Yar-Najeriya Akan Amurka Kashi Na 2


Tambra Ray
Tambra Ray

Tambra Raye Stevenson,wacce ta zabi zama 'yar-Najeriya fiye da zama Ba'amerikiya, tace a iya bincike da ta gudanar ta iya gano cewar kakannin ta da aka dauko a lokacin bayi shekaru daruruwa da suka wuce mutanen yankin, Arewacin Najeriya ne, domin kuwa a binciken nata an gayama ta dangin ta na jihar Adamawa ko Sokoto, don haka ta na iya bakin kokarin ta wajen gano tushen ta a kasar Najeriya.

Tambra, tace tayi yawo a kasashen Afrika, kuma taga abubuwa da dama wanda suka bata sha’awa da kasashen Afrika, musamman Najeriya. Tace a irin abubuwa da suka bata sha’awa da kasar Najeriya, shine gwamnatin kasar na daukar nauyin karatun ‘yan-kasa daga firamari har zuwa jami’a. Wanda ba haka abun yake a nan kasar Amurka ba, gwamnati na daukar nauyin karatun dan-kasa daga firamari zuwa sakandire ne kawai, saura kuwa kamar zuwa jami’a sai dai mutun ya dauki abun da suke cema "Student Loan" wato bashin dalibai.

Wanda kashi tamanin da biyar 85% na mutanen Amurka, na da bashin ‘yan-makaranta, hasali ma wasu sukan mutu da bashin, don kuwa basu iya biyan shi har tsawon rayuwar su. Da dama su kanyi karatu da bashin, wanda zasu dinga biyan kudin ruwa da zai sa baza su iya gama biyan bashin ba har bayan rayuwar su, wasu ma a sanadiyar bashin basu iya tabuka makan su komai a rayuwa.

Amma kuwa a kasa irin ta Najeriya, idan mutun zai yi kokari zai iya samun tallafi na gwamnati har ya kamala karatun shin a jami’a, batare da daukar bashin kowa ba. Wanda haka ma taimako ne ga ‘yan-kasa, kana sau da yawa matasa a Najeriya, kan iya zaman kan su batare da sun dogara da gwamnati ba. A sanadiyar albarkatun kasar

Bisa wadannan dalilan ne, yasa take ganin da Allah, yayi ta ‘yar-Najeriya to lallai da sai tafi kowa zama wani abu a duniya, a zamanta mace mai kokarin ganin ta taimaka ma mutane musamman wajen cin abinci mai gina jiki, da daukar al’adun na gar-gajiya. Tana da yakinin cewar idan mutane zasu dinga cin abinci da aka noma batare da samusu takin zamani ba, to lallai mutanen Najeriya, sai sunfi kowa lafiya da arziki a duniya.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG