Zirga-zirga bayan hutun karshen mako, yazama kyakkyawan abu, amma kuma mai ban tsoro. A kasar Sin ana iya cewar direbobi kan fuskanci barazana idan lokacin tafiye-tafiye yayi, musamman a lokacin hutu a kasar, domin kuwa milliyoyin mutane kanyi tafiya, wanda titin mota baya isar mutane.
Dubban masu motoci sun iske kansu cikin wani dogon layi a ranar Talata, wani titi mai layin motoci hamsin 50, ya cika makil da mutane, kamar filin ajiye motoci a kan G4 na babban birnin Beijing Hong Kong. Wannan titin na daya daga cikin hanyiyi da sukafi tarin jama’a a kasar, Wasu suna dubbin zirga-zirga jama’a lokacin hutun ne ya haddasa wannan cinkoson.
Wasu dai naganin cewar munmunan yanayi na daya daga cikin abun da ya haddasa wannan matsalar ta cinkoson, kana an saka wasu shingayen bincike da yasa aka kashe wasu hanyoyin, wanda yakamata ace akwai hanyoyi hamsin 50, amma ashirin 20, kawai aka bude. Hakan gaskiya yakawo cikasa ga matafiya da dama.