A kasar Amurka akwai mutane sama da milliyan daya da dubu dari uku (1.3M) da su ka daina karatun boko tun daga sakandare, bisa ga wasu dalilai daban-daban. Wannan rashin kammala karatu ya kan jawo rashin dace da akasarin aiyuka, kimanin kashi casa’in cikin dari (90%) da akan samu a kasar bisa rahoton, wani shafin kididdiga ya bayyana hakan. Shi ne ya assasa kamfanin Virgin Group, kuma yana da arziki da ya kai kimanin dalar Amurka billiyan hudu da dugo tara ($4.9B) dai-dai naira billiyan dari tara da tamanin (980,000,000,000.)
Duk da ba kammalla karatun boko ne kadai hanyar cimma buri da nasara a rayuwa ba, sau da dama mutane kan bar makaranta amma su zama wani abu a rayuwa, musamman idan suka dauki wata hanya wadda za ta kai su ga nasara a rayuwa. Wani da ya bar karatun boko tun ya na dan shekaru goma sha biyar (15) da haihuwa, ya kafa kamfani a yanar gizo mai suna Tumblrdavidkarp.com Ya bayyana irin cigaban rayuwa da ya samu duk da cewar ya bar makaranta a matakin sakandare. A lokacin da ya ke zantawa da mujallar Forbes. A ganin shi yin hakan ya kawo masa rashin more kuruciyarsa kamar sauran sa’o’insa.
Ga jerin mutane na musamman da suka cimma gagarumar nasara da dukiya.Rashin kammala karatun boko tun sakandare bai jawo masu cikas ba. Kowane yaro na da irin baiwar da Allah ya yi ma shi a rayuwa, amma abun la'akari da shi a nan shi ne, kada mutun ya ce ba zai yi karatu ba, kuma ya zamana ba shi da wani tunanin wani cigaba a rayuwa.